Ƙa'idojin Tsare Sirri

Ma'aikatar Derek Prince na mutunta bayanan ku kuma ta na ɗaukar su da muhimmanci. Mun tsara wannan ƙa'ida yadda za ta zama da sauƙin karatu, a bayyane kuma a fili tare da jaddada sadaukarwar mu ga kare sirrin ku wanda mu ke ɗauka da muhimmanci.

Wannan sanarwar ta shafi duk bayanan da aka tattara ta wannan gidan yanar gizon.

Na gaba ɗaya

Ma'anar mu na bayanan sirri shine duk wasu bayanan da za a iya amfani da su don gano mutum(misali suna, adireshi, lambar waya, adireshin imel da sauransu).

Ƙa'idar Ma'aikatar mu ce mu ɗauki duk matakan da su ka dace domin tabbbatar da ganin cewa an tsare dukan bayyanan ku da ke a hannun mu da kuma yin aiki da su a cikin gaskiya da yadda doka ta tsara dai dai da ƙa'idojin kariyar bayanai da suka dace da dokokin tsare sirri a yankunan da mu ke aiki.

Bayanan da Ma'aikatar ke tarawa da ga wurin ku

Lokacin da kuka ziyarci wannan gidan yanar gizon, za a iya tambayar ku wasu bayanai game da kan ku wanɗanda suka haɗa da Suna, adireshi da wasu bayanai na musamman.

Ma'aikatar za ta iya tattara bayanan yadda ku ke amfani da wannan gidan yanar gizon da kuma bayanai game da ku ta wurin imels, wasiƙu ko kuma fom fom da a ka cika aka aika.

Kukis

Kamar yawancin gidajen yanar gizon da ka ke ziyarta, Gidan yanar gizon mu zai yi amfani da kukis domin inganta ƙwarewar ka ta wurin sa wannan gidan yanar gizon ya tuna da kai. Wannan zai iya zama a lokacin shigar ka ko shiga ta gaba (domin tunawa da abubuwan da ka fi so, da dai sauransu).

Gidan yanar gizon mu na buƙatar wasu kukis domin ba ka damar zagayawa tsakanin shafuka da kyau kuma domin tunawa da masu amfani waɗanda suka shiga cikin shafin; misali, idan ka shigar da bayanan shiga sa'an nan ka koma wani shafin, ba za a sake tambayar ka ba saboda kukis ɗin suna gaya wa gidan yanar gizon cewa ka riga ka shiga.

Muna kuma amfani da kukis domin tantance irin zirga zirgar da ake yi a wannan yanar gizon, misali, ainihin wurin da kake, irin burauza ko kuma irin wayar da ka ake amfani da ita, shafukan da aka ziyarta, kuma da tsawon lokacin da aka ɗauka a kowane shafi. Duk wannan bayani na taimaka mana ne wajen gyara ayyukan mu da gyara gidan yanar gizon mu domin inganta ƙwarewar ku.

Wasu lokuta, Gidajen Yanar Gizon waje waɗanda ke gudanar da abubuwan da aka haɗa na iya saka kukis a cikin shafin da ku ke kallo kamar su YouTube, Soundcloud da sauransu. Ba mu da iko a kan yadda a ke yaɗa waɗannan kukis ɗin. Sai ku dubi shafukan yanar gizon ɓangare na uku domin ƙarin bayani game da waɗannan.

Me zai faru idan ba ka son a saka kukis?

Idan ka na so ka ƙayyade ko kuma ka toshe kukis da wannan gidan yanar gizon ta saka ko wasu gidaje na waje suka saka, za ka iya yin haka ta wurin burauzar ka. Akwai wurin samun taimako a cikin burauzar ka da zai taimake ka da yadda zaka yi wannan.

A maimakon haka, za ka iya ziyartar www.aboutcookies.org wanda ya ƙunshi cikakkun bayanai na yadda a ke yin wannan a n̏a'ukan bincike iri iri. Za ka kuma sami cikakkun bayanai game da yadda a ke share kukis daga na'urar ka da ƙarin cikakkun bayanai game da kukis.

Domin bayani akan yadda za ka iya yin wannan a burauzar ka, za ka buƙaci ka dubi takardar bayani na wayar ka.

Yadda Ma'aikatar ta ke amfani da Bayanan Sirrin ku.

Ma'aikatar za ta iya amfani da bayanan sirrin ka domin waɗannan dalilai: sa ido da samar da hanyar shiga shafukan yanar gizo, tallace-tallace da lissafin kuɗi, karɓar gudummawa, kiyaye bayanan membobi da bincike na fasaha da kuma kasuwanci. Ta wurin yin amfani da wannan gidan yanar gizon, ka na amincewa da a yi amfani da bayanan sirrin ka kamar hakan.

Bangare na uku da bayyanawar Bayanan Sirri

Ma'aikatar na iya bayyana Bayanan ka na Sirri ga Bangare na uku waɗanda ta ba umurnin aiwatar da Bayanan Sirri a madadin ta domin waɗanan dalilan da aka ambato a sama. Ana buƙatar waɗannan Ɓagare na uku da su amince za su yi amfani da Bayanan ka domin dalilan da ma'aikatar ta tsara sa'annan su ɗauki matakan da suka dace don hana shiga ciki saboda yin amfani ba tare da izni ba. Ta wurin yin amfani da wannan gidan yanar gizon, ka na amincewa da yin amfani da Bayannan ka kamar yadda aka ambata.

Ma'aikatar za ta iya fallasa ko bayar da Bayanai waɗanda suka haɗa har da Bayanan ka na Sirri a inda dokoki ko ƙa'idoji suka buƙaci yin haka.

Hanyoyin Haɗin waje

Wannan sanarwar ba ta shafi Gidajen Yanar Gizon waje ba. Muna ba da shawarar a dubi ƙa'idojin kowane gidan Yanar Gizon da aka ziyarta.

Dubi Google reCAPTCHA (ko ire-iren su)

Gidan Yanar Gizon mu na iya amfani da kayan aikin wasu Gidajen Yanar Gizo na waje kamar su Google reCAPTCHA domin ƙara inganta tsaro da kuma hana zirga zirgar da ba izini. Waɗannan kayan aikin za su iya tattara bayanai dangane da huldar ku da Gidan Yanar Gizon mu, kamar adireshin IP da kuma ɗabi''a don sanin ko mai ziyarar mutum ne ko kuma wata na'ura ce mai sarrafa kanta.

Domin ƙarin bayanai, a dubi Ƙa'idojin Tsare Sirri na masu samar da kayan aiki dabam-dabam.

Samowa, gyarawa ko kuma sabunta Bayanan Sirrin ka

Za ku iya gano bayanan ku da ke a hannun Ma'aikatar mu ta wurin rubuto mana wasiƙa. Haƙƙin Ma'aikatar ne ta caji kuɗi domin wannan aiki kuma ta nemi ƙarin bayanai daga gare ku, idan da buƙata.

Idan akwai wani bayani da ke hannun Ma'aikatar game da ku wanda ba daidai ba, ko na buƙatar sabuntawa, ko kuna son Ma'aikatar ta share wani bayani ko kuma a canza yadda Ma'aikatar ke tuntuɓar ku, sai ku aika da buƙatar ku ta wurin aika emel.

A tuntuɓe mu