Samun Rai Madawwami

Derek Prince
Published: 2008
Last Updated: August 2026
Read Time: 2
Lokacin da ka bayyana kanka tare da Almasihu a cikin mutuwarsa, binnewa, da tashinsa daga matattu, ikon zunubi a rayuwarka ya karye. An 'yantar da kai daga bauta da laifinsa don ka sami damar raba rayuwar tashinsa daga matattu ta har abada.
A yau, za mu duba sinadaran da ke cikin "Abubuwan da littafin Romawa Ya Kunsa." sosai. Romawa ta 6 ta gabatar da abubuwan da suka haɗa mu da Yesu. Na farko, "mun mutu ga zunubi" (aya ta 1) lokacin da Yesu ya mutu, muka kuma haɗu cikin mutuwarsa. Lokacin da aka gicciye Yesu, an gicciye "tsohon mutum namu" (aya ta 6), halin tawayen da muka gada daga Adamu, an gicciye shi. Na biyu, "an…. bizne mu tare da shi" (aya ta 4). Ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, mun mutu an kuma bizne mu tare da shi. Na uku, "mun haɗu tare da shi a cikin tashinsa" (aya ta 5). Muna tare da shi cikin mutuwa da biznewa, mun shiga cikin rayuwarsa ta tashi daga matattu, muna yin rayuwa tare da Shi. Sakamako na zahiri, da kuma ci gaban wannan haduwa da Yesu a cikin mutuwarsa, biznewa, da tashinsa daga matattu su ne kamar haka:
- "An kawar da jikin zunubi" (aya ta 6). Mugun halin da ke bautar da mu kuma yake sa mu yin laifi ko a lokacin da muke son yin abin da ya dace an raunana shi. An kashe shi.
- Saboda haka, ba za mu ƙara zama... bayin zunubi ba (aya ta 6). Zunubi ba zai ƙara tilasta mana yin munanan abubuwa masu cutarwa da lalatarwar da za su kawo mana bala'i a ƙarshe ba, a nan duniya da kuma har abada.
- Sannan kuma, an "'yantar da mu daga zunubi" (aya ta 7). An baratad da mu a zahiri, ko kuma an 'yantar da mu. Yesu ya ɗauki hukuncin zunubanmu gaba ɗaya; babu abin da ya rage. Da shike an 'yantar da mu daga ikon laifi da zunubi, yanzu muna da lamiri mai kyau kuma za mu iya tsayawa a gaban kursiyin Allah mai iko duka ba tare da tsoro ba.
- A ƙarshe, "za mu kuma rayu tare da shi [Kristi]" (aya ta 8). Wannan alƙawari ne mai girma! Za mu yi rayuwa ta tashinsa daga matattu tare da shi har abada. Ya mutu sau ɗaya ga zunubi; Ba zai sake mutuwa ba. Yana rayuwa ga Allah har abada, kuma mun sami wannan rai madawwami.
*Prayer Response
Na gode maka, Yesu, saboda aikinka a kan gicciye. Ina furta cewa ta wurin tarayya da Yesu, babu wani abu da zai sa in ƙara zama bawa ga zunubi. An mai da Yesu zunubi da zunubina domin in zama mai adalci da adalcinsa. Amin.

Zazzagewar Kyauta
Ana samun wannan ibada don saukewa, bugawa da rabawa don amfanin kai ko coci.
Zazzage PDFLambar: WD-B097-111-HAU


