Ɓoye tare da Kristi

Derek Prince
Published: 2008
Last Updated: September 2026
Read Time: 2
Gicciyen Almasihu shi ne ƙofa zuwa wani mazauni na asiri na cikakken tsaro wanda duniya ba za ta iya gani ba. A nan, rayuwarka tana ɓoye tare da Almasihu cikin Allah, wanda hakan yana sanya ka cikin cikakken aminci da kāriya ko mene ne kake fuskanta.
Yayin da muka fara duban gicciye, mukan yi watsi da shi. Amma gicciyen Yesu shi ne ƙofar zuwa ɓoyayyen wuri wanda babu dabbar da za ta iya ganowa, babu tsuntsun da zai iya gani, kuma dukan sauran halittu ba su sani ba (dubi Ayuba 28:7–8). Yana cikin wuri na ruhaniya ne. Bulus ya ce:
"To, da yake an tashe ku tare da Kristi, sai ku nemi abubuwan da ke a sama, inda Kristi yake a zaune a dama ga Allah. Ku kwallafa ranku ga abubuwan da suke sama, ba a kan abubuwan da suke ƙasa ba. Gama kun mutu, ranku kuwa a ɓoye yake a gun Kristi cikin Allah. Sa'ad da Kristi wanda wanda yake shi ne ranmu ya bayyana, sai ku ma ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka." (Kolosiyawa 3:1–4)
Muhimman kalmomi, "ranku a ɓoye yake a cikin Kristi cikin Allah," ba yana magana a kan duniya mai zuwa ba, amma a nan a yanzu haka. Zama a ɓoye tare da Kristi cikin Allah yana nufin kasancewa a wurin da ya ke a ɓoye. Asirin shi ne cewa lokacin da Yesu ya mutu, bai mutu domin kansa ba; Ya mutu ne domin mu a matsayin wakilinmu, ya ɗauki laifinmu da hukuncinmu a kansa.
Bisa ga fahimtarmu ta wurin bangaskiya a cikin Littafi Mai Tsarki, mun san cewa lokacin da Yesu ya mutu aka kuma tashe shi, to, mun mutu an kuma tashe mu. Mun ratsa mutuwa zuwa wata duniya da hankali ba zai fahimta/rarrabe wa ba, halitta kuma ba za ta iya fahimta ba. Muna cikin Kristi, kuma muna cikin Allah; babu abin da zai iya taɓa mu sai ya bi ta wurin Allah da kuma ta wurin Kristi. Muna nan cikin jiki, amma ranmu ba ya cikin wannan duniyar da ake gani. Za mu iya shiga cikin matsaloli da damuwa da yawa a cikin waɗannan santalolin yumɓuna, amma muna da rai madawwami, marar lalacewa, wanda ba za a iya hallakawa ba. Wannan shi ne cikakken tsaro. Koda menene zai zo, a cikin Kristi muna ɓoye kuma cikin ɓoyayyen wuri na Maɗaukaki, an kare mu daga dukan lahani da dukan haɗari (dubi Zabura 91:1–2). Kuma ƙofar ɓoyayyen wurin shi ne gicciye.
*Prayer Response
Na gode maka, Yesu, saboda aikin ka a kan gicciye. Ina furta cewa ta wurin gicciye, na shiga ɓoyayyen wuri na Maɗaukaki. An kare ni daga dukan cuta da haɗari, domin Yesu ya mutu da mutuwa ta domin in sami ransa. Amin.

Zazzagewar Kyauta
Ana samun wannan ibada don saukewa, bugawa da rabawa don amfanin kai ko coci.
Zazzage PDFLambar: WD-B097-117-HAU









