Mai bada Albarkar

Derek Prince
Published: 2008
Last Updated: September 2026
Read Time: 2
Labarin bawan Ibrahim a cikin Tsohon Alkawari ya bayyana muhimmiyar rawar da Ruhu Mai Tsarki yake takawa a rayuwar mai bi a yau. Shi ne kaɗai mai gudanar da gādonmu daga wurin Allah Uba, kuma ta wurinsa ne kaɗai za mu iya samun kowace albarka da aka yi alkawarinta a cikin Almasihu.
Ruhu Mai Tsarki shi ne mai bada dukan gadon "albarkar Ibrahim" (Galatiyawa 3:14). A cikin Farawa 24, mun sami labari mai kyau wanda ke nuna wannan gaskiyar. Labarin ya fada mana yadda Ibrahim ya nemo wa ɗansa Ishaku amarya. Misali ne mai sauƙi mai kyau kuma wanda ke ɗauke da muhimman mutane huɗu, uku daga cikinsu sune kamar haka: Ibrahim, wanda ke wakiltar Allah Uba; Ishaku, ɗan Ibrahim, wanda ke wakiltar Ɗan Allah tilo, Yesu; da kuma Rifkatu, amarya, wadda ke wakiltar Ikkilisiya (amaryar Kristi). Akwai wani mutum guda ɗaya, kuma, wanda, shi ne ainihi a ciki. Wannan mutumin shi ne bawan da babu sunansa, wanda ke wakiltar Ruhu Mai Tsarki. Idan muka karanta surar da tunanin waɗannan mutanen a cikin zuciya, wannan zai bayyana mana cikakkiyar gaskiyar.
Ka lura cewa a farkon surar, ya ce duk abin da Ibrahim ya mallaka yana ƙarƙashin ikon bawan. Shi ne mai kula da dukan dukiyar Ibrahim mahaifin Ishaku da kuma ɗan. Haka Ruhu Mai Tsarki yake; Shi ne mai kula da komai na Allah Uba. Mu magadan Allah ne kuma magada ne tare da Yesu Kristi. Amma mai kula da gadonmu shi ne Ruhu Mai Tsarki. In ba tare da Ruhu Mai Tsarki ba, ba za mu iya karɓa ko jin daɗin gadonmu ba.
Saʻad da Littafi Mai Tsarki ya ke magana a kan gadonmu a matsayin mu na 'ya'yan Ibrahim, yana magana ne musamman ga karɓar alƙawarin Ruhu, wanda shi kaɗai ne zai iya kai mu cikin dukan albarkar da take gadon mu. Albarkar Ibrahim tana "cikin dukan abubuwa" (Farawa 24:1), amma mai bada albarkar shi ne Ruhu Mai Tsarki. Daga nan ne Bulus ya yi magana ta musamman a cikin Galatiyawa game da karɓar alƙawarin Ruhu.
*Prayer Response
Na gode maka, Yesu, saboda aikin ka a kan gicciye. Ina furta cewa mai ba da gadona shi ne Ruhu Mai Tsarki, kuma na karɓi alƙawarin Ruhu ta wurin bangaskiya - "albarkar Ibrahim" a cikin dukan abubuwa- saboda an maida Yesu la'ana domin in shiga cikin albarkar. Amin.

Zazzagewar Kyauta
Ana samun wannan ibada don saukewa, bugawa da rabawa don amfanin kai ko coci.
Zazzage PDFLambar: WD-B097-124-HAU









