Samin amsoshin tambayoyin da aka fi yawan yi game da Ma'aikatar Derek Prince da ƙoƙarin mu na koyar da Littafi Mai Tsarki a duniya.
Ma'aikatar Derek Prince wata ƙungiya ce ta Krista ta duniya da ta bada kai wajen koyar da Littafi Mai Tsarki da kuma ƙarfafa Masu Bi don su yi rayuwa bisa ga maganar Allah. Ta na ci gaba da bayyana koyarwasa ta wajen litattafai, murya, bidiyo da kuma kayan aiki na zamani.
A waɗansu lokuta ana nufin Derek Prince Ministries (Ma'aikatar Derek Prince)
Ma'aikatar Derek Prince ta fassara koyarwar sa a cikin harsuna fiye da 100 a ƙasashe fiye da 45 a cikin nahiyoyi shida. Ƙungiyoyin mu na fassarawa da rarraba koyarwar Derek Prince a rubuce, murya, bidiyo da kuma cikin radiyo.
Ƙara sani game da muhimman ayyukan mu na hidima ta wurin danna mahaɗin da ke ƙasa.
Ayyukan hidimomiDerek Prince shahararren malamin Littafi Mai Tsarki ne da aka sani a duniya baki ɗaya kuma marubuci wanda hidimar sa ta ci gaba da ƙarfafa Krista a duniya baki ɗaya. Fahimtar sa mai zurfi na maganar Allah da sadaukarwarsa ga yin bishara ta zama abin tunawa mai ɗorewa.
Domin ƙara sani game da rayuwar Derek Prince, koyarwar sa da kuma gudummawar da ya bayar, ziyarci tarihin rayuwar sa.
Tarihin RayuwaDubi shafin mu na tuntuɓa domin cikakkun bayanai.
TuntuɓaDomin ci gaba da samun sabbin labarai da bayanai daga Ma'aikatar Derek Prince, yi rajista a wurin sabunta labaran mu.
A Sadu Da MuMuna haɗa hannu da makarantu masu koyar da Littafi Mai Tsarki da na Tauhidi a duniya duka domin shirya Fastoci da Masu Bi da koyarwa ta Derek Prince. Burin mu shine tallafawa Fastoci wajen inganta hidimar su, ta hanyar yin amfani da kayayaki masu yawa na koyar da Litafin Mai Tsarki.
A waɗansu ƙasshe, muna ɗaukar nauyin taruka, a wasu kuma muna haɗa hannu da majami'u da ma'aikatu na gida. Tuntuɓi offishin Ma'aikatar Derek Prince na gida domin ƙarin bayani.
Ma'aikatar Derek Prince ba ta kafa Majami'u, maimakon muna taimaka wa shugabanin Ikilisiya wajen yaɗa bishara, almajirtarwa da kuma ci gaban Ikilisiya - kamar yadda Derek Prince ya yi. Manufarmu iri ɗaya ce: kai wa ga waɗanda ba a kai gare su ba, da kuma koyar da waɗanda ba a koyar da su ba, sau da yawa ta hanyar samar da kayan aikin koyar da Littafi Mai Tsarki kyauta.
A Ma'aikatar Derek Prince, mun ɗauki nawayar tsare bayanan ku na sirri tare da kulawa cikin mutunci. Kulawa da kuma tsare bayanan ku, ana bida su ne ta hanyar ƙa'idojin sirrin ofishin da ku ke hulɗa da shi har ma ta wurin bin dokoki da sharuɗdan da su ka dace na wannan yankin. Wannan na tabbatar da cewa ana kula da bayanan ku yadda ya kamata, kuma cikin biyayya da muhimman dokokin kasa da su ka dace.
Domin ƙarin cikakkun bayanai game da yadda ake tattarawa, yin amfani da kuma tsarewa, muna ƙarfafa ka ka sake duba cikakkun ƙa'idojin sirrin mu.
Ƙa'idojin SirriMu na samar da kayan aikin koyarwar Littafi Mai Tsarki masu yawa, wanda suka haɗa da litattafai, koyarwa ta murya , bidiyo bidiyo, abincin yini da kuma jagora na yin nazari. Ana iya samun yawancin waɗanan a kyauta ko kuma a farashi mai rahusa
Duba kayan aikiI, muna ba da kwasa kwasai na nazarin Littafi Mai Tsarki a cikin wasu harsuna domin almajircin Masu Bi da kuma zurfafa fahimtar su game da maganar Allah.
Kwasa Kwasan Nazarin Littafi Mai TsarkiI, Akwai koyarwar Littafi Mai Tsarki na Derek Prince a cikin harsuna da yawa. Idan kana neman litattafai a cikin harshe na musamman, ka dubi shagon mu na yanar gizo ko ka tuntuɓi offishin Ma'aikatar Derek Prince na wurin ku domin samun cikkaken bayani.Wadannan kayan aikin za su zama da amfani domin nazarin kan ka ko hidima a cikin al'ummar ku.
TuntuɓaShagon Yanar GizoMuna roƙon ku da ku tuntuɓi offishin mu mafi kusa don ƙarin bayani game da tsarin yin fassara da wallafa litattafan mu.
Ku tuntuɓi offishin ku na gida inda aka sayi kayan ta yanar gizo don ƙarin taimako.
TuntuɓaZa ku iya tallafa mana ta hanyar yin addu'a, gudummawar kuɗi, ko ta hanyar yin aikin sa kai. Ku tuntuɓi offishin ku na gida don samun cikakkun bayanai yadda za ku tallafa mana da kuma haɗa hannu da mu.
Ba da gudummawa.A cikin ƙasashe da yawa, gudummawar da a ke ba Ma'aikatar Derek prince na rage haraji. Ku dubi offishin ku na gida don samun bayanai na musamman.