Kalmomi 30 masu ƙarfi
Kowace kalma ta haɗa da sunan littafi ko wa'azi.

Addu'a ba ta da iyaka. Ita ce babban makamin yaƙin mu mai kaiwa nesa. Za mu iya jefa ta daga ko'ina kuma mu sa ta kai ko'ina.
An Fallasa Shaiɗan
Ruhu Mai tsarki ya san hanyar, domin shi ne ya tsara taswirar.''
Za Ku Karɓi Iko
Daga zuciya ne al'amuran rayuwa ke fitowa. Lokacin da dokar Allah ta ke cikin zuciyar ka, ka na rayuwa yadda Allah ya ke so.''
Za ku karɓi Iko
Babu wani abu kamar yin rabin biyayya.''
Ƙofar samun albarkar Allah
“Mutumin da ya miƙa kansa ga Allah yana duba komai yadda Allah ya ke dubansa.”
Ƙofar samun albarkar Allah
Ilimi yana sanya mabuɗin a hannunka, amma bangaskiya ce ke juya mabuɗin a ƙofar kuma ya buɗe ɗakin taskar wadatar Allah a cikin Almasihu.”
Yin Shaida

“Ina ganin idan akwai abu guda da ya fi wuyar karɓa a wurin Allah, shi ne yabo da zuciya biyu.”
Shiga gaban Allah
“Kowane Mai bi yana da wata kama ta musamman na hikimar Allah da zai bayyana wa duniya, kuma yana bayyana ta ne ta wurin shaidar rayuwar sa.”
Shafuka daga littafin rayuwata
“Bisa ga tsarin Allah, aure alkawari ne inda kowane ɗayan su yake sadaukar da rayuwarsa domin ɗayan, sa'annan su yi zaman sabuwar rayuwa da juna.”
Abokan Tarayya na Rayuwa
“Addu’a cewa ‘MulkinKa shi zo’ na nufin sadaukarwa ga daidaituwa da duk abin da ya shafi zuwan mulkin.”
Sake gane Ikkilisiyar Allah
“Babbar matsalarmu a matsayin mu na ’yan adam ita ce ba mu fahimci yadda muke da daraja ba.”
Dokokin Aiki
“Kada ka ƙaskantar da kanka, domin Allah yana ɗaukar ka da dajara. Ya bada jinin Yesu domin ka.”
Manufar yin Gwaji
“Allah har yanzu yana ji da kyau. Yin tuba da watsar da zunuban mu yana sake buɗe hanya zuwa gare Shi.”
Za Ku Karɓi Iko

“Ra’ayin da ake da shi game da aure a kowace al’ada ko wayewa, yawanci alama ce ta gaskiya da ke bayyana ainihin ɗabi’u da yanayin ruhaniya.”
Allah Mai Haɗa Aure Ne
“Yin naciya, hanya ce ta musamman, ta samun abu mafi kyau na Allah.”
Karɓar Abu Mafi Kyau daga wurin Allah
“Darasin shi ne: dole ka kasance mai yafewa. Ba ayi adalci ba, bai kamata ba, zalunci ne! To sai me? Allah ne ya shirya shi haka. Shi ne mai iko. Wannan ita ce bangaskiya!”
Ikon Ba da Kai
“Rayuwar Krista ba kawai jin daɗi da kiɗan goge ba ce. Duk wani Krista da ya miƙa kansa zai ga cewa yaƙi na cikin abin da zai ɗanɗana a rayuwarsa.”
Yaƙi a Cikin Sama
“Ɓata 'ya'yan ku ba alheri ba ne. Sau da dama, babu shakka, alamar ragwanci ce. Yana sauki a lalatar da 'ya'ya da a horar da su.”
Mazaje da Ubanni
“Wacce ce hanyar shiga hutu? Jin muryar Allah. Wannan shi ya sa muke da Krista masu damuwa da yawa. Ba su san yadda za su ji muryar Allah ba.”
Ku Kula da Kanku (Sashi na 1)
“Ƙwayar maganar: yin shaida. Sa'ad da Yesu ya mutu, na mutu. Sa'ad da aka binne Shi, aka binne ni. Sa'ad da ya tashi, na tashi. Gaskata cewa na karɓi adalci daga wurin Allah ta wurin bangaskiya.”
Tafiya zuwa Roma

“Yesu ne matattarar rayukan 'yan Adam. Makomarsu ta har abada ta danganta ne da wurin da su ka tsaya da Yesu.”
Ƙarshen Rayuwa
“Akwai abubuwa uku da dole ka yi don karɓar baftismar Ruhun Mai Tsarki: ka ji ƙishi, ka zo wurin Yesu, ka sha.”
Za ku karɓi iko
“A kowane lokaci da ka yanke shawara mai kyau, kana ƙarfafa ɗabi'a mai kyau kuma kana gina hali mai kyau.”
Za ku karɓi iko
“Na gaskata cewa yana da muhimmanci ƙwarai a gare mu duka mu gane cewa zunubi na farko a duniya ba kisa ba ne, ba zina ba ne, amma girman kai ne.”
Yaƙi a cikin Sama
“Bai kamata mu bar abubuwan da ba mu gane ba su toshe mana wuraren sanin gaskiya inda Allah ya bayar da fahimta mai kyau.”
Yaƙi a cikin Sama
“Ba za mu iya kasancewa na Allah ba idan ba mu kasance a shirye domin bauta masa ba. Allah ba ya marabtar lalatattu masu son kai a gidansa.”
Yaƙi a cikin Sama
“Daukar giciye na nufin mika son zuciyar mu.”
Ƙofar samun albarkar Allah

“Halin ka game da kuɗi a gaskiya yana bayyana halin ka game da Allah da kansa.”
Shirin Allah domin Kuɗinka
“Bangaskiyar ƙwarai ta Littafi Mai Tsarki na fitowa ne daga zuciya kuma ta na nuna yadda rayuwar mu take. Ba kawai wani ilimin kai ba ne, ko kuma nishaɗin zuci; amma ainihin wani ƙarfi ne mai aiki a cikin zuciya.”
Bangaskiya ta yin Rayuwa
“Halin da muke ginawa a cikin wannan rayuwa shi zai ƙayyade yadda za mu kasance a har abada. Wata rana za mu bar baye-bayen mu a baya; halinmu zai kasance tare da mu har abada.”
Bagaskiya ta Yin Rayuwa