Labarai Daga Ko’ina a Duniya

Ta wurin samun ƙarfafawa daga koyarwar Derek Prince, muna samun shaidu daga Fastoci, shugabannin Ikkilisiyu da Masu Bi daga ko'ina cikin duniya a kai a kai. Gano dalilin da ya sa Ma'aikatar Derek Prince ta kasance amintacciyar hanyar ƙarfafawa da koyarwar Littafi Mai Tsarki domin Masu Bi a ko'ina tun shekara ta 1971.

Abin da Mutane ke Cewa

An ja hankalina zuwa ga koyarwar Derek Prince watanni kaɗan da suka gabata. Ba zan iya gode masa don abubuwan da na koya ba. Na sami sabuwar fahimta a cikin abubuwan ruhaniya. Ina jin sa a kowace rana kuma ina gode wa Ubanmu na Sama domin koyarwar sa.''

Carmen M, France

Sunan Derek Prince ya zamanto sunan da a ke haɗa wa da amincin da ƙafin hali na yin magana akan batutuwan da yawancin masu wa'azi ke jin tsoron su yi tunani akai ballantana ma su koyar.''

John Hagee, Wanda ya kafa Hagee Ministries

Ina kallon Derek Prince a kan manhajar YouTube na tsawon wasu shekaru har zuwa yau. Ya na yin koyarwa tsantsa kuma mai wartsakarwa wanda har yanzu ya na da tasiri a cikin koyarwar sa a lokacin da koyarwa tsantsa ta yi wuya.''

Minerva O, United States.

Ina cike da matuƙar mamaki na ikon Allah da ya yi aiki a cikin rayuwar Derek Prince, ta yadda jagorancin sa ya kawo canji cikin harkokin duniya ta wurin addu'ar Derek da biyayyarsa wadda ta kawo farkarwa a cikin rayuwar mutane da yawa. Ƙaunar Allah da nufinsa game da Derek kuma ta wurin wannan mutumin ta ɗauke zuciya ta.''

Phil Keaggy, Award-Winning Musician and Recording Artist.

Na koyi abubuwa da yawa daga koyarwar ku.''

Pastor Lazarous P, Zambia

(Derek Prince) jagora da Uban bangaskiya ga miliyoyin mutane ne. Kamar dai Annabi Elisha, mutuwar sa ta zama ƙwayar da a ka shuka a ƙasa wadda ke ci gaba da ba da rai. Babbar daraja ce saduwa da shi fuska da fuska, kuma da gaske zan iya cewa mutumin nan da ke ɗauke da wannan hidimar, mutum ne mai ban mamaki.''

Kimberley Daniels, Kimberley Daniels Ministries International

Ina sauraron koyarwar Derek Prince kuma ta canza rayuwa ta. Na gode wa ma'aikatar Derek Prince.''

Susannah T, Australia

Koda yake na sami lambobin yabo na ilimi guda biyu da wasu makamantansu da yawa, saduwa da Yesu da kuma samun shi a cikin rayuwa ta shine abu mafi muhimmanci da ya taɓa faruwa da ni. Kuma samun Derek Prince a matsayin aboki da malami ya ba ni babbar ƙauna, murna da salama. Har ila yau, ina amfani da kalaman Derek a cikin nazari na na Littafi Mai Tsarki a kowane wata.''

Al Kasha, Academy Award-Wining Composer-Songwriter

Rayuwata ta canza ta wurin koyarwar Derek Prince.''

Miriam G, United States

Ingantaccen shugabanci irin na Manzanni na Derek Prince na gaskiya da tasiri na tsawon rayuwar sa, ya bar ingantattun abubuwa, zurfin fahimta da adalcin ruhu a cikin gurbin da ya bari na koyarwa da gargaɗi.''

Jack W. Hayford, President of International Church of the Foursquare Gospel and Chancellor of The King's College and Seminary

Ina ci gaba da samun albarka da ƙarfafawa daga Ma'aikatar Derek Prince. Na gode domin kun sa samun koyarwar Derek mai zurfi ta zama a sauƙaƙe''.

Lynne C, United States

Derek Prince babba ne a wurin hidimar kuɓutarwa; babu shakka ya na gaba da lokacin sa. Shi da ya ke matacce, ya na magana har yanzu, amin.''

Greg Lock, Founder of Global Vision Bible Church

Ina son wannan aikin hidimar. Na sami 'yantarwa daga hannun maƙiyi.''

Patrice A, Trinidad and Tobago

Ana gane Ubannin bangaskiya ta wurin rijiyoyin wartsakarwa da suka haƙa da kuma ta wurin bagadin hadayar da su ka gina. Kamar yadda ya ke a zamanin da, haka kuma ya ke a wurin mu a yau. Gimshiƙan gaskiya na rayuwar Krista na nuna cewa mun sami kasancewar Uban bangaskiya a zamanin mu. Mutum mai irin wannan marmari na ruhaniya ne ya haƙo gaskiyar da ke cikin wannan wurin, mai hazaƙa cikin ilimi da kuma fahimta mai sabonta rayuwa waɗanda sune suka zama rijiya da bagadi domin wannan zamani mai matuƙar buƙata. Bari Allah ya ba mu matasa masu kwazo kamar sa.''

Stephen Mansfield, Author of 'Derek Prince - A Biography'

Na ci karo da ɗaya daga cikin koyarwar Derek Prince a manhajar YouTube. A duniya, muna cewa 'da tsautsayi', amma na san wannan ba tsautsayi ba ne. Na gaskata cewa jagoranci da bishewar Ruhu Mai Tsarki ne ya ja ni zuwa ga dukan gaskiya. Wannan ya fara ne kusan wata daya da ya gabata kuma tun daga lokacin na ci gaba da kallo a kowace rana.''

Lisa J, United States

Ba a wuce gona da iri ba idan an ce duniya ba za ta iya biyan Derek Prince ba. Rayuwar sa da gurbin da ya bari ya zarce nahiyoyi da zamanu. Rubuce-rubucen sa na dabam na ɗaukar abubuwan ruhaniya a waɗansu lokuta masu wuya, ta wurin ɗanɗano (na kansa), wato, (Derek) na fassara abubuwan ruhaniya da masu wuya. A cikin duniyar da ke cike da litattafan taimakon kai, na sihiri da na ƙa'idoji da ɗabi'un mutane,ya samar da wuri da murya da ke kawar da mu daga lumewa cikin labaru yayin da muke hallaka a cikin rashin hikima. Waɗanda suka fara tafiyarsu ko suka ci gaba a cikin wannan aikin hidima ta Derek Prince sun kyautatawa kan su. Bari ku ci gaba a cikin koyarwar manzanni, ba yin gudu kaɗai ba amma ku yi nasara a cikin tseren da ke gaban ku.''

Michael Pitts, Connerstone Global Network

Na kasance da albarka sosai daga Derek Prince Ministries. Koyarwarku a bayyane take kuma ni mai sauraro ne na yau da kullum.

Darryl L, Amurka

Muna tuna lokacin da Derek Prince ya yi magana a cikin majami'ar mu. Abin girmamawa ne karɓar baƙuncin wannan mutumin Allah mai daraja...''

Kehilat HaCarmel, Carmel Congregation

Na gano wa'azin Derek Prince a lokacin da aka yi kulle na annoba kuma ina jin salama da farin ciki yayin da na ke sauraron koyarwar sa.

Meing, Malaysia

Ya kasance muradin zuciyar Derek ya lura da waɗanda ke da buƙata kuma da yin juyayi domin ɓatattu.''

Barry Segal, President and Co-fouder, Vision for Israel

An yi mani baftisma a makarantar sakandare kuma na shiga sosai cikin bin addinin Krista, duk da haka ban san aikin Almasihu a kan giciye domina ba ne. Na yi tunanin cewa waɗansu ne su ke da buƙatar Yesu amma ba ni ba. Na yi rayuwar zunubi. Bayan waɗansu shekaru, na gaji da rayuwata marar amfani kuma na so wata tafiya ta gaske. Na kalli dukan bidiyoyi masu ƙarfafawa da na iya samu amma babu wata salama mai dorewa a ciki na. Bayan wani lokaci ina nema, sai na yanke shawarar in nemi fuskar Allah da gaske. Wata rana na durƙusa a ɗakina kuma na roƙi Allah gafara, na sake fara karanta Littafi Mai Tsarki kuma. Allah ya bi da ni zuwa Romawa 10:9-10 kuma ya ba ni bangaskiyar karɓa. A ƙarshe na san abin da Yesu Almasihu ya yi mani a kan giciye. Godiya ga Allah! Ta hanyar tashar ku ta YouTube na sami koyarwa mai yawa da ta ƙara mani bangaskiya, kuma suna da matuƙar amfani ga tafiya ta tare da Kristi.

Samuel Z, Taiwan

Muna tunawa da Derek Prince da ƙauna mai yawa da kuma girmamawa...''

Alison Eastwood, National Director, Ebenezer Operation Exodus

Rayuwata ba za ta taɓa zama ɗaya ba bayan sauraron koyarwar Derek Prince. Shekaru biyu ke nan yanzu kuma na jajirce gaba ɗaya a tafiyata, magana da tunani. Ɗaukaka ga Allah! Na gode.

Shawnda J, United States

Marmarin Derek na zama Uba har yanzu gurbi ne mai ɗorewa ga Ikkilisiya kuma misali ne da sauran shugabannai za su bi.''

Cheryl Wilcox, Christian Broadcasting Network

Derek Prince malami na ne. Ina koyo daga gare shi kowace rana. Ya kasance abin albarka a rayuwata kuma ina godiya ga Ubangijimmu don wannan. Na gode!

Carmen R M, France

Ma'aikatar Derek Prince ta kasance jagora a ɓangaren yaƙin ruhaniya da koyarwa a kan al'amuran ruhaniya bisa ga fahimtar Krista. Tare da offisoshi 45 a cikin duniya, wannan Ma'aikatar ta sami karɓuwa, kaiwa da kuma tasiri a duniya na tsawon shekaru masu yawa.''

RMI Media

Na gode da hidimar ku mai ɗorewa ga duniya. Na kasance ina sauraron koyarwar Derek Prince mafi yawan lokacin shekarar da ta gabata. Irin wannan abin ƙarfafawa ne.

Daniel, Birtaniya

A wasu shekaru da suka gabata na kasance ina neman wani da zai iya koyar da ni Kalmar Allah da gaggawa. Har zuwa lokacin ban sami kowa ba kuma duk abin da na sani ya fito ne kawai daga karatu. A wannan lokacin na kasance ina neman Allah kuma ina bincika YouTube, inda na samo koyarwa daga Derek Prince. Na cika da mamaki. Tun daga lokacin na kasance ina kallon bidiyon sa a kullum.

Bruno S, Portugal

Derek Prince ya buɗe idanu na ta hanyar koyarwarsa kuma ya zama misali da zan bi.

Lucinda, United States

Ni da Mata ta mun gano koyarwar Derek a manhajar YouTube kuma wannan ya taimaka mana sosai wajen fahimtar yaki na ruhaniya. Yanzu mun sami 'yanci kuma muna ci gaba da tafiya cikin bangaskiya tare da Yesu.''

Pietro P, Switzerland

Ina godiya ga Allah domin Ma'aikatar Derek Prince. Kun kasance a wurin da ya dace a lokacin da ya dace.''

Charles M, United States

An haife ni cikin iyalin Hindu amma na karɓi Yesu Almasihu a matsayin Ubangiji na da Mai Cetona wasu shekaru da suka gabata. Tun lokacin nan na gano Derek Prince a YouTube kuma na warke daga ciwon damuwa. Na koyi abubuwa da yawa kuma na samo amintaccen malamin Littafi Mai Tsarki (bayan dogon bincike). Na gode wa Ma'aikatar Derek Prince sosai don yaɗa Kalmar Allah da Bishara a duk duniya.''

Shreyas J, India

Yau ce rana ta farko da na kalli wa'azi daga Derek Prince. Ya kasance abin karfafawa sosai. Na gode.''

Theresa, United States

Na sami albarka sosai daga koyarwar Derek Prince.''

Annamma Q, India

Ina godiya ga Allah domin Ma'aikatar Derek Prince. Albarka ce samun irin waɗannan koyarwa masu zurfi da ke zuwa kai tsaye cikin zuciya.''

Ann M P, United States

Wani ɗan lokaci da ya wuce nayi ƙoƙarin karanta Littafi Mai Tsarki amma ban fahimta ba saboda da fassarar da na ke da ita ta King James Version ce. Ban san cewa akwai wasu fassarori ba. Ashe ina cike da jahilci sosai. Saboda haka na yi ƙoƙarin neman Ikkilisiyar da zan je, domin na yi tunanin cewa lallai za a koyar da ni kuma za su iya bayyana mani. Na je wurare da dama kuma na ƙarasa da takaici. Babu wani kusa da ni da zai iya nuna mani hanyar. Saboda haka na fidda zuciya ! Kwanan nan ina kallon YouTube sai na ci karo da Derek Prince. Yanzu na shaƙu da shi! Shi ne irin mutumin da nake nema. Ina godiya sosai cewa bidiyoyin sa har yanzu suna nan kuma ana fassara su. Ina koyon abubuwa da yawa! Ina kallon bidiyon sa kowace rana.''

Belisa G, USA

Ina samun ƙarfafawa soasi ta wurin wa'azin Ma'aikatar Derek Prince. Burina ya ƙaru wurin koyon Maganar Allah da kawo albarka cikin iyalinmu. Na gode domin dukan kayan aikin da ku ka samar.''

Pilli B, India

Koyarwar Derek Prince ta canza rayuwata. Yanzu ina rayuwa tare da ƙarin sanin abubuwan ruhaniya fiye da da. Ina farin ciki da kasancewa a wannan sabuwar tafiya tare da Ruhu Mai Tsarki. Koyo game da la'ana da albarka ya zama kamar yadda Allah ya sa zai kasance. Har ta wurin bidiyo na yanar gizo na Derek Prince, ina jin kasancewar Allah da ƙarfi a ɗakina. Annabi na gaskiya kuma mutumin Allah. Ina jiran in gaishe shi kuma in gode masa a Sama!''

Suzie Grace, United Arab Emirates

Ina gode wa Derek Prince domin cikakkiyar koyarwarsa! Kaunar sa, haƙurin sa, da sadaukarwar sa sun kasance sanannu sosai tun daga farko! Ya koya mani abubuwa da yawa! Ya na ɗaya daga cikin masu wa'azin da nake sauraro! Allah ya yi magana ta hanyar sa kuma ya taimaka mani wajen buɗe idanuna ga gaskiya!''

Elizabeth, Canada

Derek Prince