Bayarwa domin tunawa

Bar kyauta a cikin wasiyarka.

Tunawa da Derek Prince Ministries a cikin wasiyarka hanya ce mai kyau don faɗaɗa Mulkin Allah da barin tunawa mai dorewa.

Zuba jari cikin yin almajiranci

Ba lallai sai ka zama mai arziki kafin ka bar wani abu don tunawa ba amma mun fahimci cewa da farko za ka so ka yi wa masoyan ka tanadi. Amma, ka tabbata cewa komai girma ko ƙankartar kyautar ka zata zama abin godiya, kuma a hannuwan mu, zata haifar da 'ya'ya a rayukan Krista da Ikkilisiyu da yawa a duniya. Duk irin kyautar da ka bayar, za ta taimaka sosai ga wanda yake buƙata.

Koyarwar Derek Prince ta canza rayuwata ta hanyoyin da ban taɓa tsammani ba. Fata na shine cewa tsarar da ke zuwa nan gaba za su sami wannan damar don ɗanɗana tasirin canza rayuwa na kalmonin Derek. Wannan shine dalilin da ya sa na zabi barin kyautar tunawa ga Derek Prince Ministries. Na san wannan kyautar za ta taimaka wajen ci gaba da koyarwar Derek, ta ci gaba da shafar rayuka na shekaru masu zuwa, koda bayan mun je sama.''

Kyautar ku ta tunawa na iya ba Krista masu jin yunwar ruhaniya damar samun koyarwar Littafi Mai Tsarki da za su iya amfani da ita don samun ikon sauya rayuwa na Kalmar Allah a cikin rayuwarsu, ikklisiyu da yankunan su.

Yadda kyautar ku ta tunawa ke yin tasiri a cikin rayuka

  • Kyautar ku ta tunawa na iya sa koyarwar Derek ta kasance kyauta ga sabbin tsara na Krista a duniya.
  • Kyautar ku ta tunawa na iya tabbatar da cewa an fassara da buga koyarwar Derek a cikin sabbin harsuna don karfafa Masu Bi a ko'ina.
  • Kyautar ku ta tunawa na iya taimakawa wajen tanada kayan aikin don ƙirƙirar kayan almajiranci na zamani da yin wa'azi.
  • Kyautar ku ta tunawa na iya shirya Fastoci na gaba, daliban makarantar Littafi Mai Tsarki da masu wa'azi don zurfafa bincike cikin Kalmar Allah da maida sabbin tuba su zama almajirai.

Yadda za ka sa mu a cikin wasiyar ka

Ma'aikatar Derek Prince

Ƙungiyar Agaji Mai Rajista

Idan ka rigaya ka rubuta wasiyar ka, ka na iya canzawa ta wurin cika cordicil form ɗinmu

Codicil form

A tuntube mu don ƙarin bayani. Muna ba da shawarar ka tattauna da iyalinka akan niyyarka da kuma tuntubar lauya don cikakkiyar shawara game da doka.

A tuntuɓe mu
Colin Dye