Logo
Logo
Koya
LittattafaiKwasa kwasan nazarin Littafi Mai TsarkiKayan Aiki
HidimomiGame da
Najeriya Flag Icon

Menu

  • Gida
  • Koya +
    • Hidimomi
    • Game da +
      • Haɗa Hannu +
        • Tuntuɓa +

            Samu eBook kyauta

            Fara tarin Derek Prince tare da eBook kyauta lokacin da kuka yi rajista ga wasiƙarmu.

            Koyarwar Littafi Mai Tsarki Kyauta
            Logo
            Logo
            GidaKoyaHidimomiGame daBa da gudummawa

            Haƙƙin Mallaka © 2026 Ma'aikatar Derek Prince. An kiyaye duk haƙƙoƙin

            TuntuɓaSirriHaƙƙin MallakaLasisiTaswirar Yanar Gizo
            Rai Madawwami, A Yalwace | Derek Prince Ministries

            Trending Resources

            Shahararrun koyarwa suna yin tasiri a yau

            Addua Domin Gwamnati
            Addu'a Domin Gwamnati
            *Read

            Akwai Harsuna

            Addu'a Domin Gwamnati

            Wasikar Koyarwa

            Koyi yadda Krita za su iya yin tasiri a kan alʻamuran duniya domin ɗaukakar Allah ta wurin yin addu'a da karɓar alƙawur

            Furta Kalmar Allah
            Ruhunsa Mai Tsarki a Cikin Mu
            *Listen*Read

            Akwai Harsuna

            Ruhunsa Mai Tsarki a Cikin Mu

            Nazari

            Ta yaya za mu ci nasara a kan jiki? Allah yana ba mu iko ta wurin Ruhunsa amma dole ne mu zaɓi mu yi amfani da shi.

            Furta Kalmar Allah
            Cika Sharuɗɗan Allah
            *Read

            Akwai Harsuna

            Cika Sharuɗɗan Allah

            Nazari

            Ba za mu iya samun alherin Allah ta wurin kokarinmu ba, amma dole ne mu cika sharuddansa. Koyi abin da ake nufi da zama ...

            Furta Kalmar Allah
            Mai bada Albarkar
            *Read

            Akwai Harsuna

            Mai bada Albarkar

            Nazari

            Wani bawan da ba a ambaci sunansa ba a cikin littafin Farawa ya bayyana aikin Ruhu Mai Tsarki wajen kawo mana gadonmu da...

            Furta Kalmar Allah
            Jin Daɗin Albarkar
            *Read

            Akwai Harsuna

            Jin Daɗin Albarkar

            Nazari

            Nufin Allah shi ne ka bauta masa da farin ciki saboda yalwar da yake bayarwa, ba wai ka rayu a ƙarƙashin la'ana ba.

            Furta Kalmar Allah
            Alherin Allah a fannin Kuɗi
            *Read

            Akwai Harsuna

            Alherin Allah a fannin Kuɗi

            Nazari

            Yaya alherin Allah yake aiki? Kyauta ce da ake karba ta wurin bangaskiya ga Yesu Almasihu, wadda ba za a taba samunta ta...

            Furta Kalmar Allah
            “Alƙawarin Ubana”
            *Read

            Akwai Harsuna

            “Alƙawarin Ubana”

            Nazari

            Ruhu Mai Tsarki shi ne babban alkawarin Allah, kyauta ce da ake karɓa ta wurin bangaskiya, wadda kuma aka saya da jinin ...

            Furta Kalmar Allah
            Samun Ɗaukakar Sa
            *Read

            Akwai Harsuna

            Samun Ɗaukakar Sa

            Nazari

            Yesu ya dauki mafi zurfin kunyarmu a kan Gicciye. An fallasa shi domin a tufatar da mu da daukakarsa madauwamiya.

            Furta Kalmar Allah
            Kula da Matalauta
            *Read

            Akwai Harsuna

            Kula da Matalauta

            Nazari

            Yadda muke bi da matalauta yana bayyana abin da ke cikin zuciyarmu. Littafi Mai Tsarki ya ce ba su taimako rance ne kai ...

            Furta Kalmar Allah
            Farin Cikin Da Aka sa A Gabansa
            *Read

            Akwai Harsuna

            Farin Cikin Da Aka sa A Gabansa

            Nazari

            Yesu ya jimre wa kunyar gicciye saboda farin cikin da aka sa a gabansa. Wannan farin cikin kuwa shi ne na kawo ku zuwa g...

            Abubuwan da aka Bayyana

            Sabbin albarkatun da aka nuna yau da kullun

            Gida
            Kayan Aiki
            Furta Kalmar Allah
            Rai Madawwami, A Yalwace

            Rai Madawwami, A Yalwace

            Derek Prince

            Derek Prince

            A So
            Raba
            Hausa

            Akwai Harsuna

            Gabatar da Shaida

            Tayi

            Bayar

            Published: 2008

            Last Updated: September 2026

            Read Time: 2

            A matsayinsa na Makiyayinmu Nagari, Yesu yana ba da rayuwa mai cike da cikakken tsaro da yalwa ga waɗanda suke binsa gaba ɗaya. Ka fahimci ma'anar karɓar rai madawwami da yake bayarwa, rayuwar da ba za mu taɓa halaka ba, kuma babu wanda zai iya ƙwace mu daga hannunsa.

            Yesu ya kira kansa "makiyayi mai kyau" (Yahaya 10:11, 14). Za a iya taƙaita tanadin makiyayi, kamar yadda aka nuna a Zabura ta 23, a cikin kalma ɗaya mai girman gaske: cikakken tsaro. Amma ku tuna cewa ana ba da dukan tanaje-tanajen gwargwadon miƙa kanmu ne. Idan miƙa kanmu cikakke ne, tsaronmu ma cikakke ne. Idan akwai karanci na miƙa kai, to, ba za mu iya samun cikakken tsaron da Yesu yake bayarwa ba.

            Za mu iya ƙarfafa wannan misali na Tsohon Alƙawari ta hanyar duban kalmomin Yesu a cikin Sabon Alƙawari:

            "Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata, da kisa, da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace" (Yahaya 10:10)

            Yesu yana gaya mana dalilin da ya sa ya zo cikin duniya. Ya taƙaita shi da wata kalma mai sauƙi: cewa "za mu sami rai." Ba rai ɗan kaɗan ko taƙaitacce ba, amma rayuwa "yalwatacciya." Rai mai yalwa. Rai ga kowane fanni na rayuwarmu. Rai da zai wadaci kowane ƙalubale da kowacce damuwar da ke gabanmu.

            Bayan haka, a gaba kaɗan, Yesu ya yi amfani da kalmar nan, “rai madawwami”:

            "Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na; ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su hallaka ba har abada; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna." (Yahaya 10:27–28)

            Lura da ƙwayar maganar: "Ina ba su rai madawwami, ba za su hallaka ba." Bisa ga wannan ayar, mun ga cewa Yesu ya zo ne domin mu sami rai madawwami, ran da ya zarce wannan duniyar. Ran da ya zarce kabari. Ran da ya ke madawwami. Na taɓa jin wani ya yi wannan sharhi mai zurfi: "Na gaskata cewa zan rayu tare da Allah domin Allah ya zama raina." Wannan shi ne irin ran da Yesu ya zo ya ba mu - na har abada.

            *Prayer Response

            Na gode maka, Yesu, saboda aikin ka a kan gicciye. Ta wurin mutuwarka, ina da rai madawwami a yalwace, domin Yesu ya mutu da mutuwata domin in sami ransa. Amin.

            Nayi Sallah
            A So
            Raba
            Expand Content
            Ad Image

            Zazzagewar Kyauta

            Ana samun wannan ibada don saukewa, bugawa da rabawa don amfanin kai ko coci.

            Zazzage PDF

            Lambar: WD-B097-118-HAU

            Kyauta
            Bayar
            Ba da Ra'ayin ku