“Alƙawarin Ubana”

Derek Prince
Published: 2008
Last Updated: September 2026
Read Time: 2
Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da dubban alkawuran Allah, amma Yesu Almasihu ya ware guda ɗaya sama da duka a matsayin Alkawarin Uba. Gano yadda wannan babbar albarka, wadda aka saya ta wurin hadayarsa a kan Gicciye, ake bayarwa kyauta gare ka ta wurin bangaskiya kaɗai.
Karɓar baiwar Ruhu Mai Tsarki ga Mai Bi bai dogara a kan wata cancantarsa ba; ya dogara ne kaɗai a kan wadatacciyar hadayar Kristi. Ta wurin bangaskiya ne, ba ta wurin ayyuka ba, "ta wurin bangaskiya muka karɓi Ruhun nan da aka yi alƙawari" (Galatiyawa 3:14).
Wannan ra'ayin ya yi daidai da kiran ƙarshe da Yesu ya yi wa almajiransa kafin hawansa sama:
"Ga shi, ni zan aiko muku da abin da Ubana ya Alƙawarta. Amma ku dakata a birnin tukuna, har a yi maku baiwar iko daga sama" (Luka 24:49)
Yesu na magana ne game da baftisma cikin Ruhu Mai Tsarki da almajiran za su karɓa a ranar Fentikos.
Maganar nan "Alƙawarin Ubana" tana ba mu fahimta mai ban mamaki game da tunani da manufar Allah Uba game da baiwar Ruhu Mai Tsarki. Wani ya mori ra’ayin riƙau (conservative) ya yi ƙiyasin cewa Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi alƙawura iri dabam dabam har dubu bakwai waɗanda Allah ya ba wa mutanensa masu bada gaskiya. Amma daga cikin waɗannan, Yesu ya ware ɗaya kawai daga cikin sauran a matsayin na musamman: alƙawarin Ruhu.
Bulus ya kira wannan "albarkar Ibrahim" (Galatiyawa 3:14), ta haka ya haɗa shi da babban manufar Allah wajen zaɓen Ibrahim domin kan Sa. Lokacin da Allah ya fara kiran Ibrahim daga Ur, Ya ce:
"Zan sa maka albarka... domin ka zama sanadin albarka... dukan duniya za su sami albarka" (Farawa 12:2–3)
A cikin ci gaba da yin mu'amala da Ibrahim, Allah ya ƙara tabbatar da manufarsa sau da yawa.
"Zan albarkace ka... Ta wurin zuriyarka dukan al'ummar duniya za su sami albarka" (Farawa 22:17–18)
Duk waɗannan alƙawuran Allah suna duban kalmomin Bulus: “alƙawarin Ruhu” (Galatiyawa 3:14). Yesu ya zubar da jininsa a kan gicciye domin ya sayi wannan albarkar, wadda aka yi alƙawarin ta ga zuriyar Ibrahim.
*Prayer Response
Na gode maka, Yesu, saboda aikin ka a kan gicciye. Ina furta cewa Yesu ya zubar da jininsa a kan gicciye domin ya sayi albarkar Ibrahim—abin da ya kira “Alƙawarin Ubana”—kuma na karɓi alƙawarin Ruhu Mai Tsarki mai albarka, domin an maida Yesu la'ana domin in shiga cikin albarkar. Amin.

Zazzagewar Kyauta
Ana samun wannan ibada don saukewa, bugawa da rabawa don amfanin kai ko coci.
Zazzage PDFLambar: WD-B097-125-HAU









