Kawar da La'anar

Derek Prince
Published: 2008
Last Updated: September 2026
Read Time: 2
Wani babban wahayi mai iko daga Ruhu Mai Tsarki yana nuna yadda Yesu ya kawar da kowane fanni na la'anar talauci a kan Gicciye. Ya ɗauki yunwarmu, ƙishirwarmu, tsiraicinmu, da dukan rashinmu domin mu sami albarkar wadatar Ibrahim a cikin kowane abu.
Yesu ya ɗauki la'anar talaucin mu, wadda aka gabatar mana da su gaba ɗaya a cikin Maimaitawar Shari'a 28:48:
"Domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku, za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci."
A waɗansu shekaru da suka wuce, yayin da nake yin wa'azi a kan batun tanadin Allah na kuɗi, sai na sami wahayi daga Ruhu Mai Tsarki wanda ya zarce komai a cikin bayanan wa'azin da na shirya. Yayin da nake tsaye a gaban jama’a ina ta wa’azi, ina ganin hoton Yesu a kan gicciye a cikin tunanina. Ina ganinsa a can da kyau kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana. Ruhu Mai Tsarki ya yi mani magana a kan fannoni huɗu na la'anar talauci, ɗaya bayan ɗaya, yana nuna mani cewa Yesu ya kawar da la'anar ta kowace fuska.
Da farko, yana jin yunwa—lokacin da aka tafi da shi domin a gicciye shi, bai ci abinci ba kusan saʻoʻi ashirin da huɗu. Na biyu, ya ji ƙishirwa—“Ina jin ƙishirwa” yana ɗaya daga cikin maganganunsa na ƙarshe. Na uku, ba shi da sutura a jikin sa—sojojin Romawa sun cire masa dukan tufafinsa sun kuma raba a tsakanin su. Na huɗu, yana cikin buƙatar abubuwa da yawa—Ba shi da rigar da zai sa a lokacin da yake mutuwa, kuma ba shi da kabarin da za a bizine shi.
Yesu ba shi da komai. Me yasa? Saboda a cikin shirin Allah, Ya kawar da la'anar talauci a madadin mu. Da farko, ban fahimci cikakkiyar ma'anar abin da Ruhu Mai Tsarki ya ke nuna mani ba. Duk da haka, idan na duba baya, zan ce wannan wahayin ya ba ni tushen bangaskiya ta domin samun wadata. A cikin cikakkiyar musayar ƙarshe, Yesu ya ɗauki la'anar talaucin mu domin mu sami albarkar Ibrahim, wadda Allah ya albarkace shi" da ita a cikin dukan abu" (Farawa 24:1), wanda Ruhu Mai Tsarki ke bayarwa.
*Prayer Response
Na gode maka, Yesu, saboda aikin ka a kan gicciye. Ina furta cewa ka kawar da la'anar talauci na gaba ɗaya ta kowace fuska saboda Yesu ya ɗauki talauci na domin in sami yalwarsa. Amin.

Zazzagewar Kyauta
Ana samun wannan ibada don saukewa, bugawa da rabawa don amfanin kai ko coci.
Zazzage PDFLambar: WD-B097-127-HAU









