Sanannun alamomin La'ana

Derek Prince
Published: 2008
Last Updated: ሴፕቴምበር 2026
Read Time: 2
This teaching is not currently available in አማርኛ.
Shin akwai wasu munanan yanayi kamar rashin lafiya mai dorewa, rashin wadatar kudi, ko rugujewar iyali da suke kamar suna maimaita kansu a tarihin iyalinku? Koyi yadda za ka gane idan la'ana ce take aiki, kuma ka sami 'yanci daga ikonta ta hanyar kammalallen aikin Yesu a kan Gicciye.
Na tattara jerin sanannun alamomin la’ana guda bakwai. Yawancin la'anoni ba sa shafar mutum ɗaya kaɗai; maimakon haka, galibi suna shafar iyali ko manyan al'ummomi. Muhimmnan yanayin la'ana da albarka a bayyane suke a cikin Littafi Mai Tsarki wato, su na bi daga tsara zuwa tsara muddin dai ba a yi wani abu da zai katse su ba. Na haɗu da mutanen da matsalolinsu sun samo asali ne a ɗaruruwan shekaru na tarihin iyali.
Bisa ga abin da na lura da shi, ga alamu guda bakwai da ke nuna kasancewar la'ana a rayuwarka ko ta iyalinka. Idan kana fuskantar ɗaya daga cikin waɗannan, ba zan ce lallai akwai la'ana ba. Amma idan da yawa daga cikinsu sun bayyana a cikin iyalinka, a wurare dabam dabam da kuma cikin tsararraki da yawa, to, za ka iya tabbatar da cewa akwai la'ana. Waɗannan alamu sune kamar haka:
- Rashin hankali da taɓin hankali;
- Ci gaban wata cuta mai tsanani, musamman idan ta gado ce;
- Ci gaba da samun ɓarin ciki ko matsalolin da ke da alaƙa da mata;
- Lalacewar aure da rabuwar iyali, musamman idan akwai su a tarihin iyali;
- Rashin wadatar kuɗi, idan abin yana ci gaba;
- An san ka da "mai samun haɗari" a koyaushe; da kuma,
- Samun tarihin kashe kai cikin iyali ko mutuwa ta wani sanadi.
Ba za mu dinga magana a kan matsalar ba, amma za mu ƙarfafa samun maganin. An maida Yesu la'ana domin mu shiga cikin albarkar.
Prayer Response
Na gode maka, Yesu, saboda aikinka a kan gicciye. Ina furta cewa duk wata alama ta la'ana a rayuwata, mutuwar Yesu ita ce maganin, domin an maida Yesu la'ana domin in shiga cikin albarkar. Amin.

ኮድ: WD-B097-122-HAU









