Mamayewar Albarku

Derek Prince
Published: 2008
Last Updated: September 2026
Read Time: 2
Ka daina tone irin bangaskiyarka don ka gani ko suna tsirowa. Sa’ad da ka fara neman mulkin Allah da adalcinsa, za ka iya hutawa da sanin cewa albarkunsa ba kawai za su bi ka ba, amma a gaskiya za su riske ka.
A wani lokacin da nake a Ireland, akwai wani yaro ɗan shekara shida wanda iyayensa suka ba shi dankali ya shuka. Ya shuka dankalin na sa, bayan mako guda, sai ya je domin ya ga ko suna girma. Babu wata alamar girma. Bayan makonni biyu, bai ga komai ba dai, don haka sai ya tono su domin ya ga idan ma suna tsirowa. A ƙarshe, ya tono su kusan sau uku ko huɗu, amma ba su yi girma ba!
Waɗansu Krista ma suna kama da wannan ƙaramin yaron. Suna shuka dankalin bangaskiyarsu, sannan sai su tono su domin su ga ko suna yin girma. Dalilin bangaskiya shi ne a bar Allah ya sa mu yi girma. Muna cika sharuɗɗan, amma kuma Allah ne yake cika alƙawarin albarkatar mu. Maimaitawar Shari'a 28:2 ta ce ga waɗanda suka cika sharuɗɗan na Allah:
"Dukan albarkun nan za su sauko muku su zama naku, idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku."
Ina ƙaunar kalmar nan "mamayewa." Ba mu ne ya kamata mu yi gudu muna neman albarkar ba; su ne ke neman mu. Za mu iya kwanciya da dare mu yi ta tunani game da irin albarkun da za mu samu lokacin da muka farka da safe!
Haka nan kuma, Matta 6:33 ta gaya mana:
"Sai ku kwallafa rai ga al’amuran mulkin Allah da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa."
Ba zamu neman “abubuwan” ba; za mu nemi mulkin ne. To, daga nan, sai Allah ya ƙara mana dukan abubuwan da muke buƙata.
To, waɗannan su ne sharuɗɗan samun yalwar Allah: na farko, dole ne mu kasance da kyakkyawan nufi da halaye; na biyu, dole ne mu zama da bangaskiya; na uku, dole ne mu girmama Allah, iyayenmu, da kuma masu hidimar Allah ta wurin bayarwa; na huɗu, dole ne mu kasance da kyakkyawan tunani, magana da kuma aikatawa; na biyar kuma, dole ne mu bar Allah ya ƙara mana ta hanyar da ya zaɓa da kuma lokacin Sa. Idan muka cika waɗannan sharuɗɗan, to, zamu tabbata cewa albarkun Allah za su mamaye mu. Wannan ita ce hanya ɗaya da za mu shiga cikin albarkar Allah.
*Prayer Response
Na gode maka, Yesu, saboda aikin ka a kan gicciye. Ina furta cewa zan fara neman mulkin Allah, kuma, yayin da nake yin hakan, albarkun Sa za su mamaye ni—saboda an maida Yesu la'ana domin in shiga cikin albarkar. Amin.

Zazzagewar Kyauta
Ana samun wannan ibada don saukewa, bugawa da rabawa don amfanin kai ko coci.
Zazzage PDFLambar: WD-B097-126-HAU









